2 Corinthians 3

1Yabon kanmu ne kuma muka fara yi? Ko kuwa muna bukatar wasiƙun yabo ne zuwa gare ku, ko daga gare ku, kamar yadda waɗansu suke yi? 2Ai, ku kanku ku ne wasiƙarmu, wadda aka rubuta a zukatanku, domin kowa yǎ san ta, yǎ kuma karanta ta. 3Kun nuna cewa ku wasiƙa ce daga Kiristi, sakamakon hidimarmu, ba wadda aka rubuta da inki ba, sai dai da Ruhun Allah mai rai. Ba kuma a kan allunan dutse ba, sai dai a kan allunan zukatan mutane.

4Amincewa kamar wannan shi ne namu ta wurin Kiristi a gaban Allah. 5Ba mu da wani abin da za mu nuna cewa da iyawarmu ne muke aikin nan. Iyawarmu daga wurin Allah ne. 6Shi ya sa muka gwaninta a matsayinmu na masu hidimar sabon alkawari-ba ta rubutacciyar Dokar ba, amma ta Ruhu; don Dokar, kisa take yi, Ruhu kuwa yana ba da rai.

Ɗaukakar Sabon Alkawari

7To, in hidimar da ta kawo mutuwa, wadda an rubuta a kan allon dutse, ta zo da ɗaukaka har Israʼilawa suka kāsa duban fuskar Musa saboda tsananin haskenta, ko da yake mai shuɗewa ce, 8ashe, hidimar Ruhu ba za ta fi wannan ɗaukaka ba? 9In hidimar da take jawo wa mutane hukunci tana da ɗaukaka haka, to, lalle, hidimar da take kawo adalci za ta fi ta ɗaukaka nesa! 10Gama abin da dā take da ɗaukaka, ba ta da ɗaukaka a yanzu, in aka kwatantata da mafificiyar ɗaukaka ta yanzu. 11In kuma aba mai shuɗewa ta zo da ɗaukaka, ashe, abin da yake dawwamamme, lalle ne yǎ kasance da ɗaukakar da ta fi haka nesa!

12Da yake muna da bege irin wannan, to, muna da ƙarfin zuciya sosai ke nan. 13Mu ba kamar Musa ba ne, wanda ya rufe fuskarsa da lulluɓi, don kada Israʼilawa su ga ƙarewar ɗaukakan nan mai shuɗewa. 14Amma aka sa hankulansu suka dushe, gama har yǎ zuwa yau akwai lulluɓin nan a duk saʼad da ake karatun tsohon alkawari. Ba a kawar da shi ba, sai a cikin Kiristi ne kaɗai ake kawar da shi. 15Har yǎ zuwa yau, duk saʼad da ake karatun littattafan Musa, lulluɓin nan yakan rufe zukatansu. 16Amma duk saʼad da wani ya juyo ga Ubangiji, akan kawar da lulluɓin. 17Ubangiji fa, shi ne Ruhu, kuma duk inda Ruhun Ubangiji yake, a nan ʼyanci yake. 18Mu da ba mu da lulluɓi a fuskokinmu duk muna nuna ɗaukakar Ubangiji, ana sauya mu mu ɗauki kamanninsa cikin ɗaukaka mai hauhawa. Ubangiji wanda yake ruhu kuwa shi ne mai zartar da haka.

Copyright information for HauSRK